Kasa da sati daya da majalisar tarayya ta amince da korar tsohon kwamishinan zaben hukumar INEC a jihar Adamawa Barista Hudu Ari, ya nace kan cewa 'yar takarar jam'iyyar APC Sanata Aisha Dahiru Binani ce ta ci zaben gwamna da aka yi a 2023.
An dai dakatar da Barista Hudu Ari ne saboda ya ayyana Binani a matsayin wadda ta ci zabe ana tsaka da kirga kuri'u.
Sai dai a wani taron manema labarai da yayi a Bauchi, ya yi rantsuwa da Alkur'ani cewa yana da shaidun da za su tabbatar da cewa Aisha Binani ta kayar da Gwamna mai ci Ahmadu Fintiri na jam'iyyar PDP.
Category
Labarai