Babu wanda zai tilasta wa yankin arewa sake zaben Tinubu a 2027 - Martanin kungiyar ACF ga Ganduje


Kungiyar tuntuba ta Arewa ACF da wasu masu faɗa aji a yankin sun bayyana cewa babu wanda zai iya tilastawa yankin sake zaben Tinubu a shekara ta 2027.

Kungiyar ta yi fatali da kalaman shugaban jam'iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje inda tace babu wanda zai ci wa yankin albasa ta hanyar yin wannan ikirari.

Suna wadannan kalaman ne domin martani ga kalaman Ganduje cewa masu neman shugabancin kasar daga yankin arewa su jira sai 2031 domin yin takara, yana mai jaddada cewa Tinubu sai yayi mulki karo na biyu.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp