Babbar Kotu a Abuja ta fidda ranar fara sauraron karar da aka shigar kan Wike


Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 18 ga watan Fabrairu domin ci gaba da sauraron karar da wasu mabarata da marasa galihu suka shigar kan Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike inda suke kalubalantar kama su da tsare su. 

Tun da farko, lauyan wadanda suka shigar da karar, Usman Chamo, ya shaida wa kotun cewa har yanzu ana ci gaba da cin zarafin wadanda yake karewa a babban birnin tarayya Abuja, inda ya ce Wike na yaki da barace-barace a yankin.

Saidai Yayin da yake dage sauraren karar mai shari’a James Omotosho a ranar Talata ya sanya ranar 18 ga wata a matsayin lokacin da za fara sauraron karar 

Ya kuma ba da umarnin aikewa da takardun kotun zuwa ga Sufeto Janar na ‘yan sanda, Hukumar Tsaro ta farin kaya (NSCDC), da kuma Babban Lauyan Tarayya.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp