Babban Hafsan tsaron Nijeriya Janar Christopher Musa ya tabbatar da halaka wasu jiga jigan ‘yan bindiga guda biyu a jihar zamfara

CDS Christopher Musa

 

Babban hafsan tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa ya tabbatar da halaka wasu jiga jigan bindiga guda biyu,da suka hada da Kachalla Gwammade da Kachalla Shehu.

CDS ya bada wannan tabbaci ne a wajen rufe taron kwamandojin hadin gwiwa a ranar Juma’a.

Majiyoyi sun bayyana cewa dakarun da ke kan hanyar Magami, Dan Sadau ne suka kai farmakin tare da hadin gwiwar ‘yan banga na yankin.

Majiyar ta tabbatar da cewa sojojin sun yi artabun ne da ‘yan bindigar da suka yi nasarar halaka guda shida tare da kwato babura uku da kuma bindigogi da dama, kuma Kachalla Gwammade da Kachalla Shehu na daga cikin su.

Kachalla Gwammade, wanda aka bayyana a matsayin babban kwamandan 'yan bindigar, na daga cikin wani sansani a kauyen Chabi da ke karamar hukumar Maru, a jihar ta Zamfara.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp