![]() |
CDS Christopher Musa |
Babban hafsan tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa, ya ce Nijeriya ba za ta amince da duk wani nau'i na rashin mutuntawa daga kasashen waje ga 'yan kasarta ba.
Ya bayyana haka ne a Abuja, hedkwatar tsaron Nijeriya a ranar Laraba, ya ce Nijeriya ta cancanci girmamawa a fadin duniya.
A wajen taron shekara shekara na babbar cibiyar nazarin tsaro ta kasa da ya gudana a Abuja a ranar Alhamis din da ta gabata, Musa ya bayyana cewa da bai halarci taron ba da ofishin jakadancin Canada ya hana shi Visa.
Musa ya bayyana cewa, yayin da rabin ‘yan wasan Nijeriya suka samu damar yin tafiya, shi da wasu jami'ai da dama an hana su Visa ta shiga kasar.
Da yake nuna rashin jin dadinsa kan faruwar lamarin, mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya bayyana lamarin a matsayin rashin mutuntawa da kuma abin rashin jindadi.
Saikadaraja kanka da al umarka sannan adarajaka mudai bamuga darajjar da manyankasarmu suke yimanaba saboda kansu da iyalansu sukasani kuma dukiyar kassar ta yankasane yankasane yankasane
ReplyDelete