Ba mu da shirin hana amfani da lasifika a masallatai - Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang

 

Celeb Muftwang

Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya musanta ikirarin da ake yi cewa gwamnatinsa na shirin hana amfani da lasifika a masallatai.

Hakan ya biyo bayan yada koke a shafukan sada zumunta na neman haramta wa, wanda wani John Apollos Maton ya yi ga gwamna, kwamishinan ‘yan sanda, da kuma hukumar kare hakkin dan Adam ta kasa.

Koken dai ya haifar da cece kuce musamman a kafafen sada zumunta da na gidajen rediyon jihar.

Gwamna Mutfwang yayin da yake jawabi a yammacin ranar Juma’a a birnin Bukur, ya tabbatar wa al’ummar Musulmin jihar cewa wannan zargi ba shi da tushe balle makama, ya kuma bukace su da su yi watsi da shi.  

Ya ce gwamnati, ba ta da masaniya kan wannan batu, kuma masu yada wannan jita jita sun san ba gaskiya ba ne kuma suna kokarin kawo barna a jihar,a cewar sa ana kan binciken wadanda da ke yada wannan jita jita.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp