![]() |
Luka Modric |
Ba gaskiya bane cewa Luka Modrić ba zai iya buga wasanni 2 a jere ba dan yana da shekaru 39 - cewar kocin Real Madrid Carlo Ancelotti
Mai horar da kungiyar Real Madrid Carlo Ancelotti ya bayyana cewa Luka Modric zai iya buga wasanni 2 a jere ba tare da wata matsala ba,domin yana da kwari sossai tare da ishasshiyar lafiya a jiki ba kamar yadda ake yadawa ba.
Ancelotti ya ce zuwa yanzu kungiyar ta shirya tsaf domin amfani da dan wasan mai shekaru 39,a manyan wasannin da za ta buga a kwanaki masu zuwa domin cike gibin da take da shi na wasu 'yan wasan ta da ke ciwo.