Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi wata ganawar sirri da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a birnin Abeokuta na jihar Ogun.
Ayarin motocin Atiku sun isa dakin karatu na Olusegun Obasanjo a Abeokuta, da misalin karfe 12:36 na ranar Litinin din nan.
Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya samu tarba daga abokin Obasanjo, Otunba Oyewole Fasawe.
A cikin tawagar Atiku Abubakar din akwai, tsoffin gwamnonin jihohin Cross River da Sokoto, Liyel Imoke, Sanata Aminu Tambuwal da Sanata mai wakiltar Bauchi ta tsakiya, Abdul Ningi.