Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Godswill Akpabio ya bayyana cewa kasa da kashi 30% ne na yan kasar ke biyan haraji ga gwamnatin tarayya.
Shugaban Majalisar ya ce kuma a haka 'yan ƙasar ke tsammanin gwamnati za ta samar masu da ababen more rayuwa da sauran muhimman ayyuka.
Jaridar Punch ta ruwaito Godswill Akpabio ya bayyana hakan a ranar Litinin a wajen bude taron jin ra’ayin jama’a kan kudirin gyaran haraji da shugaban kasa Bola Tinubu ya aikewa majalisar.
Category
Labarai