Gwamnatin Nijeriya na kokarin rushe tsarin makarantun karamar sakandare JSS da babba SSS da nufin mayar da tsarin ilmi ya koma shekaru 12 ba tare da wasu rabe-rabe ba.
Gwamnatin, ta bakin ministan ilmi, Tunji Alausa, ta ce tana ba majalisar lura da ilmi ta kasa National Council of Education shawarar mayar da tsarin karatu na 12-4, maimakon na 6-3-3-4 da ake amfani da shi yanzu.