Ana hasashen Naira za ta iya kai wa 1,700 kan kowace dala a watanni shida na farkon shekarar 2025

 

Naira/Dollar

Daya daga cikin manyan kamfanonin hada hadar hannun jari, Comercio Partners Limited, ya yi hasashen cewa a watanni shida na farkon shekarar 2025 naira za ta iya kai wa 1,700 kan kowace Dala, lamarin da ake ganin ya zarce na kowane lokaci.

Daily Trust ta ruwaito cewa, a karshen makon da ya gabata, farashin Naira ya karu da N45 akan kowacce dala.

Rahoton canjin kudi a kasuwar bayan fage ya nuna cewa daga ranar Litinin, 3 ga Fabrairu, 2025, zuwa 7 ga watan, naira ta kara daraja da N40 zuwa N1,565 kan kowace dala daga N1,610.

Kamfanin Comercio Partners a cikin hasashen tattalin arziki na shekarar 2025, ya ce kasuwar canjin kudi a Nijeriya ta samu habaka sosai tun a watan Disambar bara.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp