An yi garkuwa da ma'aikaci Asibitin koyarwa na jami'ar Modibbo Adama da ke Yola a jihar Adamawa da wasu mutane 3 - Rundunar 'yan sandan jihar

'Yan sanda

 

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta tabbatar da sace ma’aikacin asibitin koyarwa na jami’ar Modibbo Adama da ke Yola, Abubakar Sadiq Umar da wasu karin mutane uku.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Dankombo Morris, ne ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an yi garkuwa da mutanen ne a kauyen Mayokila da ke karamar hukumar Jada ta jihar.

CP Dankombo ya kara da cewa lamarin ya faru ne a lokacin da wasu gungun ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka mamaye yankin da sanyin safiyar ranar Litinin 17 ga watan Fabrairun 2025 inda suka fara harbe-harbe don sanya tsoro ga mutane tare da sace Umar da wasu mutane uku.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp