Wasu ministocin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu sun fara fitowa suna kare gwamnatin daga sukar da wasu jiga-jigan 'yan adawa ke yi wa gwamnatin.
A kwanan nan an ga yadda ministan kasa a ma'aikatar tsaro ya mayar wa Rotimi Amaechi da kungiyar dattawan arewa martani, da yadda ministan harkokin waje Yusuf Tuggar ya soki kalaman gwamnan Bauchi kan gwamnatin Tinubu.
Wata majiya ta shaida wa jaridar Punch cewa ministocin na bin umurnin da aka basu ne na kare gwamnatin daga 'yan adawa.
Category
Labarai