An tsaurara tsaro a sakatariyar jam'iyyar APC ta kasa a yayin da ake shirin yin taron kwamitin zartaswar jam'iyyar


 

Shugabannin jam’iyyar APC na kasa sun hallara a sakatariyar jam’iyyar domin taron kwamitin zartaswa na jam’iyyar a babban birnin tarayya Abuja. 

An kulle dukkan hanyoyin da za su kai ga titin Blantyre na sakatariyar jam'iyyar da tawagar jami’an tsaro da suka hada da sojoji da sauran jami'an tsaro.

Hakazalika an takaita zirga-zirgar ababen hawa da na da ta al'umma a titin Blantyre, an kuma ajiye 'yan jarida a waje guda duk da fitar da jerin sunayen 'yan jarida da aka amince da su shiga wajen a safiyar yau Laraba da kamar yadda sakataren yada labarai na Jam'iyyar Felix Morka ya fitar.

Mutanen da suka isa sakatariyar da wuri sun hada da, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, ministan kasafin kudi da tsare-tsare, Atiku Bagudu da mataimakin kakakin majalisar wakilai, Benjamin Kalu.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp