A watan Janairun 2025 aka shata fara bai wa kananan hukumomin kuɗaɗensu kai tsaye, sai dai tsaiko wajen buɗe asusun ajiya ya sa an sake ɗage lokacin fara aiwatar da tsarin.
Babban bankin Nijeriya CBN ya ce dole ne kananan hukumomin su gabatar da bayanan yadda suka kashe kudadensu na shekaru biyu kafin a fara turo musu kudin kai tsaye, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.
Sai dai ana fargaba ko kananan hukumomin za su iya cika ka'ida kafin karshen watan Fabrairu domin fara karbar kudadensu kai tsaye.
Category
Labarai