![]() |
Dauda Lawal Gwamnan jihar Zamfara |
Lamarin ya faru da safiyar Lahadi, a lokacin da yaran suka je itacen girki a kusa da babban asibitin garin.
Wani dan garin na Maradun da ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar wa da DCL Hausa cewa, maharan sun je da muggan makamai a bisa babura a lokacin da suka sace yaran.
Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta hannun kakakinta,Yazid Abubakar ta ce za ta bincika ta sanar da DCL Hausa. Har lokacin hada wannan labarin ba ta sanar da mu ba.