An rufe jami'ar FUDMA bayan zanga-zangar dalibai

 


Hukumomi a Jami’ar Tarayya da ke karamar hukumar Dutsinma a jihar Katsina ta rufe jami'ar biyo bayan zanga-zangar dalibai sanadiyyar halbe wani dalibin jami'ar.

Rahotanni sun ce jami’an rundunar hadin gwiwa ta Civilian Joint Task Force da ke aiki a yankin sun halbi dalibai biyu, lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwar daya daga ciki.

Wani ganau ya shaidawa Jaridar PUNCH cewa daliban masu zanga-zanga sun tare babbar hanyar Dutsinma zuwa Katsina tare da kona tayoyi.

1 Comments

  1. Nayi tunanin zaku fada DALILIN DA yasa Daliban sukayi Zanga-Zangar din, Amma Baku fada BA. AN YA KUNSAN AIKINKU KUWA

    ReplyDelete
Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp