An rantar da sabbin shugabannin kungiyar dillalan man fetur na kasa reshen jihar Katsina

 


... Zamu zamanantar da sana'armu

Sabbin shuwagabannin hadaddiyar kungiyar dillalan man fetur ta kasa reshen jihar Katsina IPMAN, sun sha rantsuwar kama aiki bayan samun sasanci ga yan kungiyar kamar yadda kundin tsarin mulkin kungiyar ya tanada.

Yayin da yake jawabi sabon shugaban kungiyar Alhaji Aminu Ahmed AA Rahamawa ya bayyana cewa jihar Katsina ita ce jihar da tafi kowace jiha saida mai da sauki duba da irin yadda kungiyar IPMAN reshen jihar ke taka rawa wajen kyautata ma al'ummar jihar.

"Akwai yan kasuwa da suke sayar da kaya ba sa samun riba, faduwa suke, ba dan komai ba sai dan al'ummar jihar Katsina su samu sauki duba da irin yanayin halin da ake ciki".

"Zamu zamanantar da sana'armu duba da yanayin da kasuwanci ya je a kasarnan, zamu yi iya kokarin mu muga an samu canji a harkokin kasuwancinmu".

AA Rahamawa ya yi roko da gwamnati da ta samar ma kungiyar sakatariya ta din-din-din domin samun saukin aiwatar da aikace-aikacen kungiyar.

Daga karshe sabon shugaban AA Rahamawa ya bayar da tabbacin cewa akwai gagarumin sauyi da zai amfani jihar Katsina dama yan kasuwa.

Sabbin shuwagabannin sune Alhaji Aminu Ahmed AA Rahamawa a matsayin Chairman, Alhaji Danlami Shuhu El-Habib vice chairman, Alhaji Nura Gaji Daura secretary, Aminu Namadi Dankama assistant sec, Alhaji Sanusi Boda treasure, Alhaji Mas'udu Abdullahi Daura financial sec, Alhaji Salisu Sani Yaro auditor, Hassan Umar Masanawa legal advisor, Alhaji Aminu Auwal Malumfashi organizing sec, Alhaji Sagir Bello P.R.O, Alhaji Rabiu Asha-shayi P.R.O ii, Anas Mukhtar Magina admin sec, ABDULLAHI AHMED DAURA, chief whip, ALHAJI UMAR USMAN SARKI ex officer, UMAR HARUNA DAURA, ALHAJI ZAHARADDEEN (DAN MALIKI MALUMFASHI)

A yayin kammala taron an bayar da shaidar cin zabe ga kowane shugaba a mataki daban-daban, wanda al’umma da dama suka samu damar halarta.

Taron wanda ya gudana a dakin taro na Aldusar Park dake bisa titin gidan rodi a cikin birnin jihar Katsina. Ranar Alhamis 13/02/2025, ya samu halartar.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp