An kori wasu jami'an 'yan sanda uku bisa zargin rashawa da garkuwa da mutane

 

Police

Rundunar ‘yan sandan jihar Abia da ke kudu maso gabashin Nijeriya ta kori wasu jami’anta uku bisa zarginsu da rashin da’a.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Maureen Chinaka ce ta sanar da hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Juma’a.

Chinaka, ta ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Abia, Danladi Isa ne ya  bada umarnin korar jami’an 'yan sandan.

Kakakin ‘yan sandan ta bayyana sunayen jami’an da aka kora da suka hada da Jonas Nnamdi,  sai James Daniel, da Ifeanyi Emeka.

A cewar ta an kori jami'an uku ne saboda dabi'u mara sa kyau da suka hada da rashawa, hada baki, da satar  mutane ta hanyar yin garkuwa dasu.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp