Mahukuntan jami'ar Nnamdi Azikiwe dake Awka jihar Anambra sun kori dalibar nan Goddy-Mbakwe Chimamaka Precious, bisa cin kwalar wani malami tare da kama shi da fada saboda ya wuce a cikin bidiyon TikTok da take yi.
A cikin wasikar kora mai kwanan watan 13 ga watan Fabrairu 2025, dauke da sa hannun mukaddashin magatakardar makarantan Victor I. Modebelu, jami'ar ta ce dabi'un dalibar sun saba wa dokokin makarantar.
Lamarin dai ya dauki hankali sosai a cikin shafukan sada zumunta, bayan da bidiyon da dalibar da malaminta ya bayyana.
Category
Labarai