A yayin kaddamar da barikin, shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA, Mohamed Buba Marwa, ya ce barikin za ta karfafa ayyukan hukumar wajen yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi a fadin Nijeriya.
Marwa ya bayyana cewa rashin wurin zama ga jami’an hukumar NDLEA na jefa su da iyalansu cikin hadari daban-daban.
A cikin sabuwar barikin da aka kaddamar mai fadin hekta 18, akwai gine ginen manyan ofisoshi, dakunan kwana, da sauran kayayyakin more rayuwa don karfafa ayyukan jami'an hukumar NDLEA.