![]() |
Abdullahi Umar Ganduje |
Shugaban jam’iyyar NNPP reshen jihar Osun, Tosin Odeyemi, ya caccaki shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, kan shirin jam’iyyarsa na karbe Kano a zaben gwamna mai na 2027.
Tosin Odeyemi ya ce babu yadda za ai APC ta lashe zaben kano domin talakawan jihar basa tare da su,suna goyon bayan Abba Kabir Yusuf.
Da yake mayar da martani ga shugaban jam’iyyar APC na kasa, wanda ya bayyana NNPP a matsayin matacciyar jam’iyyar a Kano, Odeyemi, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce ya zama wajibi Ganduje ya farka daga dogon mafarkin da yake yi na karbar mulki a jihar.
Sanarwar ta kara da cewa babu yadda za ai al'ummar kano suyi kuskuren zaben jam'iyyar APC a nan gaba domin jihar kano na hannun NNPP.
Ya ce abin mamaki kaji wanda ke zaune a wani wuri mai nisa da jiharsa ta ya yi takamar mutane da yawa daga cikin NNPP sun shirya ficewa daga jam’iyyar zuwa APC.