![]() |
Abba Kabir Yusuf |
Gwamnatin jihar Kano ta amince da ranar Juma’a 28 ga Fabrairu, 2025, a matsayin ranar fara hutun zango na biyu a makarantun Firamare da na Sakandire a jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar ilimi ta jihar, Balarabe Kiru ya fitar ranar Talata.
Sanarwar ta ce daliban makarantun kwana za su koma makarantunsu a ranar Lahadi, 6 ga Afrilu, 2025 yayin da za a ci gaba da karatu a ranar Litinin, 7 ga Afrilu, 2025.
Sai dai sanarwar ta ruwaito Kwamishinan ilimi,Ali Haruna Makoda, yana kira ga iyaye da su kula da 'ya'yansu a lokacin da ake hutun kuma su tabbatar da bin ka’idojin ranar da za a koma makarantu.
Ya yi gargadin cewa za a dau matakin ladabtarwa a kan daliban da suka ki bin ka'ida ta komawa makaranta bayan karewar kwanakin hutun.
Makoda ya yaba da hadin kai da goyon baya da ake bai wa ma’aikatar tare da yi wa dalibai fatan samun nasarar azumin watan Ramadan ba tare da wata matsala ba.