![]() |
NDLEA |
Jami’in hulda da jama’a na hukumar, ASN Sadiq Muhammad Maigatari, ya bayyana hakan a wata hira da yayi da manema labarai a Kano, ya ce wayar da kan iyaye ya zama wajibi su duba irin alewar ake kaiwa unguwanninsu.
Ya ce an kama alewar "Choculate" amma a cikinta ana zargin an lullube ta da abubuwan da ke sanya maye.
Maigatari ya ce ana zargin ana sayar da alewa a unguwanni ga yaran da ba su sani ba, a lokacin da za su je makaranta, ya kuma bukaci iyaye da su rika lura da wasu dabi’u da ‘ya’yansu ke nunawa a unguwanni da cikin gidajen su.