Akpabio ya ba da umarnin a fitar da Sanatar Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti daga zauren majalisar dattawan Nijeriya


Zazzafar muhawara ta barke a majalisar dattawan Nijeriya, yayin da shugaban majalisar Godswill Akpabio ya umarci a fitar da Santa Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar Kogi ta tsakiya daga zauren majalisar.

Rikicin dai ya samo asali ne daga wani rahoto da babban mai tsawatarwa na majalisar dattawa Sanata Mohammed Monguno ya mika, inda ya shaidawa majalisar cewa sanata Natasha ta ki karbar sabon mukami da aka ba ta.

Kafin Monguno ya kammala maganarsa, Natasha Akpoti-Uduaghan ta ci gaba da magana ba kakkautawa, inda ta bukaci a yi mata bayani kan canjin kujerar nata kwatsam.

1 Comments

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp