Akalla mutane 14 ne suka rasu sakamakon barkewar cutar zazzabin Lassa a jihar Taraba.
Babban jami'in cibiyar lafiya ta Tarayya (FMC) dake birnin Jalingo Dr Kuni Joseph , ya bayyana hakan inda ya ce ko a makon da ya gabata mutum 6 ne suka rasu a baya bayan nan.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewar an samu bullar cutar da rashe -rashen da akayi a watanni Uku baya da suka gabata.