Zarge-zargen da hukumar EFCC ke yi wa Farfesa Usman Yusuf

 

Farfesa Usman Yusuf


Hukumar EFCC dai na zargin Farfesa Usman Yusuf da amfani da ofishinsa a lokacin yana shugaban hukumar kula da inshorar lafiya ta Nijeriya a shekarar 2016 zuwa Yulin 2017 ya sayi wata motar da zai rika hawa ta kudi sama da Naira milyan 49, da hakan ya ci karo da kasafin kudin Naira milyan 30 don sayen irin motar. Hukumar ta ce hakan ya saba wa sashe na 22 na kundin dokar cin hanci ta shekarar 2000.

Kazalika, hukumar na zargin Farfesa Usman Yusuf da cewa a shekarun 2016 da 2017 ya ba wata gidauniya mai suna GK Kanki Foundation kwangilar kudi Naira milyan 10.1 don horar da mutane 90 da hukumar ta ce a ka'idar irin wannan horarwa, mutane 45 ne yake da damar a ba su horo. 

Bugu da kari, hukumar na zargin Farfesa Usman Yusuf da amfani da ofishinsa na matsayin shugaban hukumar kula da inshorar lafiya ta Nijeriya a shekarun 2016 da 2017 don ba wani kamfani mai suna Zaramat Global Services Ltd kwangilar kudi Naira 771,428.58 don ba da horo kan yadda shawo kan bala'o'i.

Haka kuma, hukumar na zargin Farfesa Usman Yusuf da amfani da karfin ofishinsa a shekarun 2016 da 2017 ya ba wani kamfanin dan'uwansa mai suna Lukekh Nigeria Ltd kwangilar kudi Naira 17,500,000.00 da hakan suka ce ya saba doka.

1 Comments

  1. Abin dariya wallahi, wani hauka sai jami,an kasata 🇳🇬

    ReplyDelete
Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp