Za a kammala titin Kano-Kaduna- Abuja nan da watanni 14, in ji ministan yada labarai Mohammed Idris

Ministan yada labarai da wayar da kan al'umma na Najeriya Mohammed Idris Malagi, ya ce za a kammala aikin hanyar Abuja,Kaduna zuwa Kano nan da watanni 14.
Idris ya bayyana hakan ne a lokacin da yake kaddamar aikin sashen farko na hanyar daga Abuja zuwa Kaduna a Alhamis.
Ya yin duba aikin ministan na yada labaran na tare da na ministan aiyyuka Mista David Umahi, da shima ya jaddada cewar aikin zai kammala akan lokaci.
Ministan aiyyuka Umahi ya ce aikin za'a fadada shi da zai dangana da filin jirgin saman kasa da kasa Malam Aminu Kano , dake jihar Kano.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp