![]() |
Shugaba Tinubu |
Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya amince da a gina kwalejin kimiyya da fasaha ta tarayya a Gwarinpa, Abuja babban birnin kasar.
Wakilin jaridar Daily Trust ya ruwaito cewa, an sanya wa sabuwar makarantar sunan shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A wata wasika mai dauke da kwanan watan 16 ga watan Junairu 2025 da aka tura ga ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ministan ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya ce gwamnatin tarayya ta amince da kafa Bola Ahmed Tinubu Polytechnic,a Gwarinpa domin bunkasa fasahar zamani, kere-kere, sana’a da kasuwanci a fadin kasar.