Yawan ɗanyen mai da Nijeriya ke fitar wa ya ƙaru - Kungiyar OPEC


Wani sabon rahoto da kungiyar kasashe masu albarkatun danyen mai na duniya OPEC ta fitar, ya nuna cewa yawan mai da Nijeriya ke fitar wa ya karu da ganga 152, 000 a kowace rana a cikin watan Nuwamban 2024.

Rahoton da kugiyar ta fitar ya nuna cewa karin ya kai kashi 11 inda a yanzu Nijeriya ke fitar da ganga miliyan 1.486 a kowace rana, sabanin ganga miliyan 1.333 a watan Oktoban 2024.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp