Akalla mutane 18 ne rundunar 'yan sandan jihar Katsina suka ceto a hannun 'yan bindiga bayan dakile wani yunkurin garkuwa da mutane a kan hanyar Funtua-Gusau da ke jihar Zamfara.
Rundunar tace ta kuma yi nasarar kwato wasu dabbobi da aka yi yunkurin sacewa a kauyen Gidan Gada dake karamar hukumar Kafur ta jihar Katsina.
Da yake jinjinawa jami'an 'yan sanda kan wannan kokarin, kwamishinan 'yan sandan jihar CP Aliyu Abubakar Musa, ya bukaci al'umma su ci gaba da goyon bayan jami'an tsaro tare da kwarmata musu bayanai.