![]() |
'Yan sanda |
'Yan sanda a jihar Kaduna sun kama wasu mutane biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da kuma wasu ‘yan fashi da makami guda hudu a yankin Samaru da ke karamar hukumar Zariya.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Mansir Hassan ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Ya baiyana cewa an kama wadanda ake zargin ne bisa sahihan bayanan sirri da aka samu.
Mansir Hassan ya ce bayan samun bayanan sirrin da jami’an ‘yan sandan da ke Samaru a Zariya su ka yi, ba tare da ɓata lokaci ba suka kaddamar da wani samame a yankin Zango da Hayin- Jarumai da ke Samaru a Zariya, lamarin da ya kai ga kama mutane hudu da ake zargi da aikata fashi da makami.
Wadanda ake zargin sun haɗa da Abubakar Alkamu, Ahmed Isah, Hassan Isah da Umar Abubakar.
Rundunar ‘yan sandan ta ce a wani bincike da ta gudanar a gidan Hassan Isah, jami’an sun gano wata wuka da ake zargin ana amfani da ita wajen aikata miyagun laifuka na.