![]() |
Sanata Godswill Akphabio |
Shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya bukaci ‘yan kasar da su yi imani da sauye sauyen tattalin arzikin da shugaba Bola Tinubu ya zo da shi, yana mai cewa nan gaba za su ci riba.
Akpabio ya bayyana hakan ne a wajen wani taro a Jos, babban birnin Jihar Filato.
Shugaban majalisar dattawan wanda Sanata mai wakiltar Filato ta Arewa ya wakilta, Mwadkon Dachungyang, ya ce idan al'ummar Nijeriya suka ci gaba da hakuri da sauye sauyen tattalin arzikin shugaba Tinubu za a samu sauyi a nan gaba.