![]() |
Shugaba Bola Tinubu |
Gwamnatin Nijeriya ta kammala shirye shiryen raba tsabar kudi Naira 75,000 ga ‘yan kasar miliyan 70 a wani yunkuri na rage radadin fatara.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi babban mataimaki na musamman ga shugaban kasar kan harkokin al'umma, Hon. Aliyu Audu,ya bayyana cewa matakin ya dace da kudurin gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu na yakar talauci a fadin kasar.
Audu, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC, ya bayyana cewa hakan ya tabbatar da shugaba Tinubu ya nuna kwazo a cikin watanni 19 kacal da ya yi yana mulkar kasar
Ya kara da cewa jajircewar manufofin Tinubu sun samar da sakamako mai kyau, wanda hakan yasa ake ci gaba da samun masu zuba hannun jari zuwa kasar.