'Yan Nijeriya miliyan 14 ke shan magani ba bisa ka'ida ba - Daraktar hukumar NAFDAC


Daraktar Janar ta hukumar kula da ingancin abinci da magunguna a Nijeriya Mojisola Adeyeye ta ce 'yan kasar miliyan 14 ke shan magani ba bisa ka'ida ba.

Mojisola ta bayyana hakan ne a yayin kaddamar da shirin wayar da kan matasa kan illar shan magani ba bisa ka'ida da ya gudana a Fatakwal.

Ta kara da cewa, wannan matsalar na shafar iyalai da dama da al'ummar kasar.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp