'Yan Nijeriya mazauna kasashen waje sun dawo da dala biliyan 90 a gida cikin shekaru 5 - Hukumar NiDCOM


Shugabar hukumar 'yan Nijeriya mazauna kasashen waje NiDCOM, Abike Dabiri-Erewa, tace yan kasar dake zaune a kasashe daban-daban sun kashe kusan naira biliyan 60 a yayin zuwansu Nijeriya a watan Disamban 2024.

Ta bayyana hakan ne a lokacin da ta bayyana a gaban kwamitin hadaka na majalisar tarayya domin kare kasafin kudin hukumar.

Abike Dabiri-Erewa, ta kara da cewa yawan kudaden da 'yan Nijeriya mazauna kasashen waje suka dawo da su gida sun haura dala biliyan 90 a cikin shekaru 5, lamarin da ke kara taimaka wa wajen bunkasar tattalin arzikin kasar.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp