![]() |
Malam Dikko Umar Radda |
Wasu ‘yan bindiga da suka kai hari a wani babban asibiti a karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina a kwanakin baya, da suka yi sanadiyyar jikkata wani likita, sun bukaci a biya su kudin fansa naira miliyan 540 domin sako wata ma’aikaciyar jinya da wasu da aka yi garkuwa da su a yayin harin.
Daily Trust ta rawaito cewa daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su Yusuf Muhammad Mairuwa, mataimakin daraktan kula da harkokin jinya ne kuma shugaban sashin jinya na asibitin.
Wata majiya mai tushe ta shaida wa Daily Trust cewa maharan sun bukaci a biya su kudin fansa naira miliyan 270 domin sako ma’aikaciyar jinya.
Haka zalika 'yan bindigar sun bukaci karin naira miliyan 270 ga sauran ma’aikatan asibitin da wasu ma’aikatan wata masana’antar taki da aka yi garkuwa da su a kusa da asibitin a yayin harin.