Lopetegui |
An nada tsohon kocin Lopetegui mai shekaru 58 a watan Mayun shekarar 2024 bayan tafiyar David Moyes amma a hukumance ya karbi ragamar aiki a ranar 1 ga Yuli.
Kungiyar ta ci wasanni shida na gasar Premier ta kasar Ingila a lokacin da yake jagorantar ta.Cin da Manchester City ta yiwa Westham United 4-1 shi ne rashin nasara na tara a wasanni 20 na gasar kuma ya bar kulob din a matsayi na 14 a gasar Firimiyar kasar Ingila.
West Ham United tana tattauna da tsohon kocin Chelsea da Brighton "Potter" game da kulla sabuwar yarjejeniya da shi.