Wata tankin mai ta sake fashewa a titin Engu-Onitsha, ta yi ajalin mutane 11

 


Akalla mutane 11 ne suka mutu sakamakon fashewar wata tankar mai dauke da man fetur a hanyar Enugu zuwa Onitsha a ranar Asabar.

A lokacin da tankar man ta fadi ta zubar da man da ke cikinta, kafin ta fashe.

Da yake jawabi kan faruwar lamarin, Gwamnan jihar Peter Mbah ya ce wadanda suka jikkata na samun kulawar likitoci, kuma jihar za ta dauki matakin dakile afkuwar lamarin nan gaba da suka hada da tabbatar da dokar hanya da kuma gyaran hanyar gwamnatin tarayya da ta lalace.

Mbah ya jajantawa iyalan wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata a yayin afkuwar lamarin.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp