![]() |
Tiktok |
Shugaban ‘yan sandan yankin, Babar Baloch, ya ce mutumin dan shekaru 50 a duniya, ya mayar da iyalansa daga Amurka a kwanakin baya don zama a birnin Quetta da ke kudu maso yammacin Pakistan.
Shugaban ya ce mutumin, da yanzu haka yake tsare, ya amsa laifinsa na harbin ‘yar tasa a farkon wannan mako bayan ta ci gaba da ɗora irin bidiyon da iyalansa ke ganin bai dace ba, duk kuwa da cewa ya yi mata gargadi.