Uwar gidan shugaban kasa Sanata Oluremi Tinubu, ta kai ziyara ga jariri na farko da aka haifa a ranar 1 ga watan Janairun 2025 a asibitin Asokoro dake birnin tarayya Abuja.
Oluremi Tinubu wadda ta samu wakilcin uwar gidan mataimakin shugaban kasa Nana Shettima, ta bayar da kyautukka ga jarirai mace da namiji da aka haifa a sabuwar shekara.
Ta bayyana cewa gwamnati mai ci a shirye take wajen inganta rayuwar yara domin su girma su zama abin alfahari.