Ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP a zaben 2023, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya zargi wasu mutane da yace na ayyana kan su a matsayin jagororin arewa da yin katsalandan a sha'anin zaben dan takarar shugabancin kasa.
A zantawarsa da BBC Hausa, jagoran darikar Kwankwasiyya, ya yi zargin cewa hakan na kawo ci baya ga dimukradiyyar kasar tare da raba kan al'umma har ta kai ga an zabi dan takarar da bai cancanta ba.
Kwankwaso kuma tsohon gwamnan Kano ya jaddada bukatar jagororin su dauki darasi daga abubuwan da suka faru a baya tare da tsame bakinsu a duk wani sha'ani na zaben dan takara.
Category
Labarai