Tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga shugabanni a kowane mataki na gwamnati da su rika tabbatar da gaskiya da rikon amana ga wadanda suke shugabanta

 

Muhammad Buhari

Buhari ya bayyana haka ne a dakin taro na Banquet Hall da ke fadar gwamnatin jihar Katsina, a yayin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC gabanin zaben kananan hukumomin jihar a ranar 15 ga watan Fabrairu.

Tsohon shugaban kasar ya ce wadannan abubuwa na da matukar mahimmanci wajen samun daidaito a tsakanin al'umma da shugabanni da ke jagorantar su a dukkan matakai.

A nasa bangaren, Gwamna Dikko Radda, ya ce jihar ta kuduri aniyar gudanar da zabe na gaskiya, sai dai gwamnan ya umurci masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a jihar da su hada kai don tabbatar da nasarar jam'iyyar.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp