Tsohon shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan ya bukacin 'yan kasar su yi wa kasar fatan fita daga kalubalen da take ciki ba wai guduwa zuwa wasu kasashen ba.
Jonathan wanda ke jawabi a wajen wani taron kaddamar da wurin sarrafa waken soya na kamfanin CSS Group, da ya gudana a karamar hukumar Karu ta jihar Nassarawa.
Tsohon shugaban yace kasashen da 'yan Nijeriya ke kokarin zuwa mutane ne suka gina su, saboda haka ya jaddada bukatar su hada hannu domin gina kasarsu.
Category
Labarai