Tsohon kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Manchester City kuma kocinta Tony Book ya rasu yana da shekaru 90 a duniya
Bayanin hakan na kushe ne a cikin wata sanarwa da kungiyar ta Premier ta fitar a ranar Talata.
Books ya zama kyaftin din City inda ya jagoranci kungiyar har suka lashe manyan kofuna hudu, da suka hada da kofin gasar Premier ta Ingila da gasar cin kofin Turai, a karshen 1960s da farkon 1970s.