Abdullahi Abbas/Abbas Sani Abbas/Barau Jibrin |
Abbas Sani Abbas, wanda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sallama kwanakin baya tare da wasu kwamishinoni biyar, mataimakin shugaban majalisar dattawa Barau Jibrin ya karbe shi zuwa APC.
Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nijeriya Barau Jibrin tare da wasu jiga jigai a APC ciki harda shugaban jam'iyyar na Kano Abdullahi Abbas ne suka karbe shi inda suka yi masa maraba zuwa jam'iyyar su ta APC.
Barau ya ce karbar guda daga cikin jiga jigan jam'iyyar ta NNPP ba karamin nasara bace a gare su inda ya ce wannan ne zai kara bada dama domin samun makoma mai kyau ga al’ummar jihar Kano da Nijeriya baki daya.