Uwar gidan shugaban Nijeriya, Sanata Oluremi Tinubu ta bayyana kyakkyawar fatan akan gobe Nijeriya, inda ta bayyana shekara ta 2025 za ta zo da ci gaba masu yawa.
A cikin sakon sabuwar shekara da ta wallafa a shafin X, ta bukaci 'yan Nijeriya su ci gaba da hadin kai tare da kara kokari wajen gina kasar.
Remi Tinubu ta jaddada muhimmancin haɗaka tare da janyo kowane bangare wajen tabbatar da cewa kasar ta ci gaba.