![]() |
Gwamnan jihar Adawama Ahmadu Fintiri |
Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya soki manufofin tattalin arziki da shugaba Tinubu yazo da su,inda ya ce suna takurawa ‘yan Nijeriya, suna shan wahala
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin taron kwamitin sulhu na jam’iyyar PDP na kasa da gwamnonin Arewa maso Gabas suka gudanar da sauran masu ruwa da tsaki a jihar Bauchi
Wadanda suka halarci taron sun hada da gwamnonin Bauchi da Taraba, da kuma mukaddashin shugaban jam'iyyar PDP na kasa Umar Damagun.
Fintiri ya nuna rashin jin dadinsa da yadda halin tattalin arzikin kasar ke tafiya tare da kira ga gwamnatin tarayya da ta sake duba tsare-tsaren tattalin arzikinta da ke jefa ‘yan Nijeriya cikin matsananciyar wahala.