Gwamnatin kasar Amurka ta dakatar da tallafin yaki da cutar HIV da kasar ke bai wa Nijeriya da wasu ƙasashen masu tasowa, biyo bayan wata doka da Shugaba Donald Trump ya sanya wa hannu.
Tuni dai wannan dokar ta fara aiki tare da dakatar da duk wani tallafi na tsawon kwanaki 90.
Amurka na kashe dala biliyan 6.5 a kowace shekara domin samar da magani da kayan aikin da ake bukata domin yaki da cutar HIV/AIDS ga mutane miliyan 20.6.
Category
Labarai