Rahotanni sun tabbatar da fashewar tayar jirgin saman kamfanin Max Air dake dauke da fasinjoji 53 a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano dake jihar Kano.
Tayar jirgin ta fashe ne daren jiya Talata da karfe 10:57, lokacin da jirgin da ya taso daga filin jirgin sama na Murtala Muhammad dake Lagos ke kokarin sauka a Kano.
Sai dai dukkanin fasinjojin dake cikin jirgin ba wanda ya ji rauni ko asarar rai.
Category
Labarai